Gwamnatin Kano Ta Tura Jami’an Tsaro 1,050 Don Yaki da Masu Sata da Kwacen Wayoyi

Gwamnatin Jihar Kano ta tura jami’an tsaro 1,050  wurare 52 da aka fi samun matsalar kwacen  wayoyi da sauran miyagun laifuka a faɗin jihar, domin yaki da wannan matsala da ke ƙara ta’azzara.


A cewar gwamnatin, aikin jami’an zai ƙarfafa tsarin tsaron cikin gida da kuma dawowa da al'umma kwarin gwiwa, musamman a birane inda matsalar satar waya ta zama ruwan dare.

Da yake jawabi ga jami’an da aka tura , Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Musamman na Jihar Kano, Air Vice Marshal Ibrahim Umaru (mai murabus), ya tabbatar da cewa gwamnatin ba za ta yi kasa a gwiwa ba, har sai an tabbatar da cewa kowa yana zaune lafiya.

Shima da yake karin haske, Shugaban Hukumar yaƙi da shan miyagun kwayoyi da Kwacen Wayoyi a Jihar Kano, Manjo Janar Gambo Ahmed (mai murabus), ya jaddada kalaman Kwamishinan, inda ya ce gwamnati na da cikakken shiri na kawo ƙarshen waɗannan laifuka da ke gallaza wa al'umma musamman matasa.

Matsalar satar waya, wadda mafi yawan lokuta matasa da ke kan babura ke aikatawa, ta haddasa rasa rayuka, raunuka da kuma tsoratar da jama’a musamman a cikin dare da kuma wuraren taruwar jama’a.

Previous Post Next Post