Zargin Zamba: Kotun Abuja Ta Bayar Da Belin Emefiele Kan Naira Biliyan 2

 A ranar Litinin, Mai Shari’a Yusuf Halilu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya bayar da beliN tsohon Gwamnan Babban Bankin Kasa (CBN), Godwin Emefiele, a kan sabbin tuhumar da ake masa, kotun ta bayar da belin sa kan  Naira biliyan biyu (N2bn).

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ce ta gurfanar da Emefiele a gaban kotu bisa tuhume-tuhume guda takwas da suka shafi mallakar gidaje  753  da ke Plot 109, Cadastral Zone C09, Lokogoma District a Abuja, wanda aka gina su a fili mai girman 150,462.86 square meters.

Lokacin da aka karanta masa tuhume-tuhumen, Emefiele ya musanta laifin da ake tuhumar sa da shi.

Lauyansa, Mathew Burkaa (SAN), ya nemi a bayar da belin sa, kuma lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo (SAN), bai yi adawa da hakan ba, sai dai ya bukaci a cire wasu sashe daga takardar neman belin, kuma kotu ta amince da hakan.

A kunshin belin, Mai Shari’a Halilu ya jaddada cewa bayar da beli hakki ne da kundin tsarin mulki ya tanada, yana mai cewa Emefiele ya taba samun beli daga wasu alkalai biyu a baya, kuma bai karya sharuddan ba.

Sharuddan belin sun haɗa da:

  • Bayar da takardun tafiye-tafiyen sa da ke gaban Mai Shari’a Muazu a matsayin wani bangare na sharuddan belin.

  • Samar da mutane biyu da za su tsaya masa, wadanda su ne mazauna Abuja.

  • Wadanda za su tsaya masa dole ne su mallaki  filaye a yankin Asokoro, Maitama ko Wuse 2, kuma darajar kadarorin ta kai Naira biliyan 2.

  • Wadanda suka tsaya masa dole ne su dauki alkawarin kawo shi kotu a duk lokacin da aka bukata.

  • Idan ya tsere, wadanda suka tsaya masa za su fuskanci hukuncin zama gidan gyaran hali.

Kotun ta bai wa Emefiele wa’adin daga yau zuwa Laraba 18 ga Yuni, 2025, domin cika sharuddan belin, ko kuma a mayar da shi gidan yari.

An dage sauraren karar zuwa 11 ga Yuli domin ci gaba.

Tuhume-tuhumen da EFCC ke yi masa sun hada da:

  • Mallakar kadarori da kudaden da ake zargin an samo su ta hanyar da ba bisa ka’ida ba.

  • Rike biliyoyin naira a asusun kamfanoni da ba a san su da gudanar da ayyuka na gaskiya ba.

  • Takardun bogi na Power of Attorney da aka ce ya kirkira a watan Janairun 2021 don nuna cewa wani kamfani ne ya mallaki kadarorin.

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon kasa EFCC ta ce laifukan sun sabawa sassa 319, 362 da 364 na Dokar Penal Code, kuma suna da hukunci mai tsanani idan aka tabbatar da su.

Previous Post Next Post