Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya kai ziyara Asibitin Rundunar Sojin na 44 da ke Kaduna domin duba lafiyar wadanda suka tsira daga mummunan harin da aka kai a karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato, inda ‘yan asalin Kaduna suka rasa rayukansu yayin wani hari da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da dama.
Gwamnan ya bayyana cewa ya dauki alhakin bin diddigin wannan lamari da kan sa, tare da sanya ido kan yadda hukumomin tsaro ke gudanar da bincike da kokarin cafke wadanda suka aikata wannan ta’asa. Ya ce tuni an kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a harin, yayin da ake ci gaba da neman sauran da suka tsere. Ya tabbatar da cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba har sai an hukunta dukkanin masu hannu a kisan.
Kazalika, Gwamna Uba Sani, ya bayyana cewa Gwamnatin Kaduna ta dauki nauyin kula da lafiyar wadanda suka jikkata, tare da samar da kwararru don Kwantar musu da hankali (psychosocial support) wanda zai taimaka musu wajen warke da fitar da damuwa na raɗaɗin harin da kuma dawo da su cikin al’umma da iyalansu cikin kwanciyar hankali.
A bangare guda kuma a ranar Talata, Gwamnan ya jagoranci tawagar manyan jami’an gwamnati tare da tsohon gwamnan jihar, Muktar Ramalan Yero, zuwa Unguwan Dantsoho a Karamar hukumar Kudan, domin jajanta wa iyalan mutane 12 da suka rasa rayukansu a harin da aka kai a Mangu, yayin da suke kan hanyarsu zuwa bikin aure na ‘yan uwan su.