Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana cewa gwamnatin jiharsa ta kammala shirye-shiryen kafa sansanin soji a masarautar Zuru domin karfafa tsaro a yankin.
Gwamna Idris ya sanar da hakan ne a ranar Laraba yayin da ya kai ziyarar jaje a garin Tadurga da ke karamar hukumar Zuru, da kuma Kyebu a karamar hukumar Danko/Wasagum, Garuruwan da 'yan bindiga suka kai hari kwanan nan, tare da kashe mutane da yin awon da dabbobi.
Ya ce an kuma motoci masu sulke (APC) da zasu dinga gudanar da sintiri da sauran kayayyakin aiki daga Abuja zuwa Kebbi, don tallafawa wannan sabon sansani.
Gwamnan ya bayyana cewa za a fara da samar da matsuguni na wucin gadi don sojojin da za su fara gudanar da aiki a yankin, yayin da ake jiran kammala gina-ginen sansanin.
Kazalika gwamnan ya ce ba za a zuba ido ana kallon ‘yan ta’adda na cutar da rayuka da dukiyoyin al’umma ba tare da daukar mataki ba. Yace Gwamnatin sa na daukar batun tsaro a matsayin abi mafi fifiko.
Ya yi addu’ar Allah ya jiƙan wadanda suka rasa rayukansu a harin, ya kuma yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.
Gwamna Idris ya kuma bukaci al’umma da su kauce wa siyasantar da batun tsaro, da kuma guje wa yin maganganu marasa kyau a kafafen sada zumunta.
A nasa bangaren, Sarkin Zuru, Alhaji Sani Sami-Gomo II, ya nuna godiya bisa ziyarar jajen da gwamnan ya kai, tare da yaba wa da irin kokarin da yake yi wajen dakile matsalolin tsaro a masarautar.
