Gwamna Zulum Ya Yi Allah Wadai da Harin Ƙunar Baƙin Wake a Konduga

Gwamnan Babagana Umara Zulum na Jihar Borno,  ya yi Allah wadai da harin kunar baƙin wake da aka kai a ƙaramar hukumar Konduga, wanda aka danganta da 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP.



Ta cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Dauda Iliya, ya raba wa manema labarai, biyo bayan harin da ya afku da daren jiya.

Sanarwar ta bayyana cewa harin da ya auku da misalin ƙarfe 10 na dare a kasuwar kifi da ke ci har dare, inda mutane 12 suka mutu, sannan wasu 18 suka jikkata.

Zulum ya ce “Wannan ɗanyen aiki da waɗannan 'yan ta'adda suka aikata ba kawai mugunta ba ce, har ma cin zarafi ne ga ɗan Adam gaba ɗaya,”.

Ya ƙara da cewa, “Wannan aiki ne na mugunta da nufin tsoratar da al'umma da kuma ƙoƙarin karya ƙwarin guiwar al’ummar ke da shi. Amma mutanen Borno ba za su tsorata ba, kuma ba za  a karya masu ƙwarin gwiwa  ba.”

Gwamna Zulum ya yi kira ga jama’ar jihar da su ci gaba da yin taka-tsantsan tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga hukumomin tsaro. Ya ce haɗin gwiwar al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙi da ta’addanci.

Kazalika, gwamnan ya yi ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, yana mai cewa duk wani ɗan Borno mai kishin ƙasa yana cikin alhini tare da su.

Ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnati na aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaron lafiyar su da kuma hana aukuwar irin wannan mummunan lamari a nan gaba.

Previous Post Next Post