An tabbatar da mutuwar akalla mutane 24 tare da jikkatar wasu da dama a wani mummunan harin kunar bakin wake da wata Mata ta kai a garin Konduga, kimanin kilomita 36 daga Maiduguri, babban birnin jihar.
Rahoton da rundunar 'yan sanda a jihar Borno ta fitar ya nuna cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar 20 ga Yuni, 2025, Matar ta tarwatsa bam da ta ɗaura a jikinta a wajen sayar da abinci, inda jama’a da dama suka taru domin siyayya.
Majiyoyin ‘yan sanda sun bayyana cewa fashewar ta yi sanadin mutuwar Mutane 24, yayin da wasu da ba a tantance adadinsu ba suka jikkata. Ita ma Matar da ta tayar da bam ɗin ta tarwatse, sai kanta kawai aka iya ganowa.
Bayan aukuwar lamarin, hadakar jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda na sashen EOD-CBRN (Dake kula da abubuwan fashewa), da CJTF, tare da masu sa kai da mafarauta, sun kai agaji wurin da lamarin ya faru.
An killace yankin gaba ɗaya, tare da gudanar da bincike mai zurfi domin gano ko akwai wasu bama-bamai da aka boye, amma ba a gano wani abu mai haɗari ba.
An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) domin samun kulawar gaggawa, yayin da gawarwakin waɗanda suka mutu aka adana su a dakin ajiye gawa na asibitin. Bayan Likitoci a asibitin sun tabbatar da mutuwarsu.
Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa ana ci gaba da tantance sunaye da bayanan waɗanda abin ya shafa, kuma za a bada gawarwakin ga iyalansu wadanda abin ya shafa domin gudanar da jana’iza kamar yadda addini ya tanada.
Har ila yau, an ƙarfafa matakan tsaro a fadin garin Konduga domin hana yiwuwar sake aukuwar irin wannan hari.