Gwamnatin Jihar Benue ta bayyana Laraba, 18 ga Yuni, 2025 a matsayin ranar hutun aiki na musamman domin maraba da ziyarar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yanke shawarar takaita wasu daga cikin ayyukansa domin kai ziyarar ta’aziyya ga al’ummar jihar Benue, sakamakon hare-haren da suka yi sanadin asarar rayuka da dama a 'yan kwanakin nan.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakatariyar Gwamnatin Jiha, Serumun Deborah Aber, ta fitar, inda ta bayyana cewa ziyarar na da nufin jajanta wa gwamnati da al’ummar Benue bisa jerin hare-haren da suka auku kwanan nan.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa:
"An ayyana hutun domin bai wa jama’ar jihar damar tarbar shugaban kasa yadda ya kamata."
Sai dai an kayyade ma’aikatan da hutun ba zai shafa ba, da suka hada da:
Ma’aikatan lafiya
Jami’an tsaro da
Ma’aikatan bankuna da sauran ayyukan gaggawa
Sanarwar ta kara da cewa:
“An bukaci al’umma da su fito kwansu da kwarkwata domin tarbar Shugaban Ƙasa da tawagarsa yayin wannan ziyara mai muhimmanci.”
Ziyarar dai ana kallonta a matsayin wani babban mataki daga shugaban ƙasa na nuna alhini da jajantawa al'ummar jihar bisa ci gaba da rikice-rikice da kisan gillar da suka addabe ta, musamman a yankunan karkara.