Sarkin Kano Ya Shawarci Shugabanni Da Masu Ruwa Da Tsaki Su Hada Kai Don Kawo Karshen Fadan Daba

Mai Martaba Sarkin kano na 16 Khalifa Muhammadu Sunusi na II,  ya bayyana takaicinsa kan yadda ake ci gaba da fuskantar matsalar fadan daba da shan miyagun kwayoyi da  sace sacen wayoyi da ke neman zama  ruwan dare a jihar nan.

Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da yake sauraren korafe-korafen al'ummar   unguwannin Sheka,  Maidile da Ja'oji da dai sauran wasu unguwannin dake cikin birni Kano.



Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sunusi na II yace abuN takaici shine yanda zakaga yawancin masu fadan daban matasa ne Yan shekara a shirin da kad'an suke addabar mutane a yankunan su. 

Sarkin Kano na 16 ya shawarci shugabannin kananan hukumomi da Hakimai da Masu Unguwannin da Dagatai da Limamai da a hada Kai da jami’an tsaro wajen ganin  an kawo karshen fadan daban da shan miyagun kwayoyi a fadin jihar nan.

Daya daga cikin Wakilin al'ummar yankunan da abin ya fi addabar unguwar su ya  shaidawa Mai Martaba Sarki cewa yawancin fadan daban na samo asali ne tun daga  gidan adana namun daji wato gidan zoo  inda ake yin wasannin na gala da sauran wasannin.


Previous Post Next Post