Gwamnatin Jihar Kano Ta Ayyana Alhamis, 26 Ga Yuni, A Matsayin Ranar Hutun Sabuwar Shekarar Musulinci, 1447 AH

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana Alhamis, 26 ga Yuni, 2025, a matsayin ranar hutu domin bikin sabuwar shekarar Musulunci ta 1447 bayan Hijira.



Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya al’ummar Musulmi murnar ganin sabuwar shekara, wadda ke farawa da watan Muharram a matsayin watan farko a kalandar Musulunci wadda ke bin tsarin watanni sama (lunar calendar).

Gwamnan ya bukaci jama'ar jihar da al’ummar Musulmi gaba ɗaya da su yi bitar ayyukansu na shekarar da ta gabata, tare da karfafa addu’o’i domin tabbatar zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban jihar da Najeriya baki ɗaya.

Ya kuma kara jaddada cewa gwamnatinsa na da cikakken kudurin inganta rayuwar al'umma ta hanyar sauraron muradun talakawa da ci gaba mai dorewa.

Ana fatan wannan hutu zai ba wa jama’a dama su gudanar da ibada da kuma nazari kan rayuwa.

Previous Post Next Post