Gwamnatin Kano Za Ta Dasa Itatuwa Miliyan Biyar Don Yaƙi da Sauyin Yanayi

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana shirin ta na dasa itatuwa miliyan biyar a faɗin jihar a wani yunkuri na tabbatar da dorewar muhalli da rage illolin sauyin yanayi.

Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar da ya kai  Cibiyar Reno da Shukar Itatuwa da bada horas ga Ma’aikata ta Mai Nika da ke ƙaramar hukumar Gwarzo.


A cewarsa, wannan babban shiri na dasa itatuwa na da nufin yaƙi da hamada, hana zaizayar ƙasa, kyautata iska da muke shaka da kuma inganta kasa  birane da kauyukan da ke faɗin jihar.

Dakta Hashim ya ƙara da cewa gwamnatin Kano na da niyyar dakile tabarbarewar muhalli da ke addabar sassa da dama na jihar tare da inganta  muhalli mai cike da korayen bishiyu domin habaka lafiyar al'umma.


Previous Post Next Post