Rundunar ‘yan sanda a jihar Neja ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da yunkurin garkuwa da mutum a Minna, babban birnin jihar, tare da kwato bindiga kirar gida da wasu makamai a hannunsu.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Wasiu Abiodun, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Minna ranar Talata.
Ya ce jami’an ‘yan sanda na ofishin Tafa ne suka kama waɗanda ake zargin bayan samun kiran gaggawa daga wasu al’umma a ranar 13 ga Yuni da misalin ƙarfe 8 na dare.
Abiodun ya ce "Mutanen biyu, masu kimanin shekaru 28 da 30, sun shiga harabar wani gida a kauyen Kata kusa da New-Bwari inda suka yi ƙoƙarin sace ‘yar uwar wani mutum,".
Abiodun ya ce jami’an sun garzaya wurin da abin ya faru kuma suka yi nasarar cafke mutanen da ake zargi a wurin.
An kama su da bindiga kirar gida, wu'ka'ke biyu, na’urar sadarwa (walkie-talkie), alburusai biyu, wayoyi hannu hudu, kati cirar kudi a Banki ATM guda ɗaya, na’ura mai amfani da lantarki gudaa biyu (electric tasers), abin fesawa a ido mai yaji (pepper spray) da kuma wasu kayayyakin tsafi.
Yayin bincike, wadanda ake zargin sun amsa laifinsu, inda suka ce sun shirya sace matar ne domin neman kuɗin fansa.
Ya ce "Sun kuma yi ikirarin cewa dukkan kayan da aka kama a hannun su, sun saya ne daga wani shima mai gudanar da irin wannan aiki da ke riƙa nuna kansa a matsayin Civilian JTF,".
Ya ƙara da cewa ana cigaba da gudanar da bincike a kansu kuma za a mika su ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha domin cigaba da bincike da kuma gurfanar da su a gaban kotu.