Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta bayyana damuwarta kan rikicin da ke ci gaba tsakanin Isra’ila da Iran, tana mai gargaɗi cewa “ayyukan kai hare-hare na rashin tunani da tsari” na iya haifar da karin rikice-rikice da ka iya faɗaɗa zuwa sauran yankuna.
Ministan harkokin wajen UAE, Sheikh Abdullah bin Zayed Al-Nahyan, ya ce dole ne a dakatar da rikicin nan da take, yana mai kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da Kwamitin Tsaro su shiga tsakani don hanaci gaba da zubar da jini.
https://www.krmhausa.com/2025/06/harin-israila-kan-iran-barazana-ne-ga.html
https://www.krmhausa.com/2025/06/yarima-mohammed-bin-salman-da.html
Ministan ya bayyana cewa babu mafita da ta fi tattaunawa ta hanyar diflomasiyya, yana mai jaddada muhimmancin amfani da hikima, tuanani da bin doka da girmama ikon ƙasashe wajen warware rikicin.
UAE ta kuma nuna adawa da hare-haren jiragen saman Isra’ila kan Iran da martanin makamai daga Iran zuwa manyan biranen Isra’ila, tana kira da a dakatar da wannan hare-hare na tashin hankali domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin duniya.