Gwamnatin Iran ta bayyana shirinta na kare kanta ta hanyar fito da cikakken ƙarfin ta a yayin da rikicin da ke faruwa tsakaninta da Isra’ila ya shiga rana ta shida, lamarin da ke ƙara tayar da hankula a yankin Gabas ta Tsakiya.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Kasar, Esmaeil Baghaei, ya ce a halin yanzu Iran tana mayar da hankali ne kacokan wajen kai hari kan wuraren sojin Isra’ila. Sai dai ya gargadi Amurka da kada ta tsoma baki a rikicin, inda ya ce hakan zai iya janyo “yakin fito na fito gaba ɗaya”.
Wannan furuci na zuwa ne bayan tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi nuni da yiwuwar shiga rikicin, lamarin da ya biyo bayan tura jiragen yaki zuwa yankin.
Tun daga fara musayar hare-haren makamai tsakanin ƙasashen biyu a makon da ya gabata — wani abin da ba kasafai yake faruwa kai tsaye ba — duniya ke ci gaba da kira da a dakatar da rikicin, yayin da tsoron bazuwar yaki a fadin yankin ke ƙaruwa.