Ayatollah Ali Khamenei, shugaban addinin kasar Iran, ya bayyana cewa kasarsa ba za ta amince da kiran Shugaban Amurka Donald Trump, ya yi na ta mika wuya ba ba tare da wani sharadi ba.
Cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin din Kasar a ranar Laraba, Khamenei ya ce babu wata kasa da za ta iya tilasta zaman lafiya ko yaki a kan Iran. Wannan na zuwa ne a karo na farko da ya yi tsokaci tun bayan harin da Isra’ila ta kai wa Iran a ranar Juma’a.
Khamenei ya ce “Ina sanar da duniya cewa mutane masu basira da suka san tarihin Iran da al’ummarta ba za su taba yi mata barazana ba, domin ba za ta mika wuya ba,”.
Ya gargadi Amurka da kada ta kuskura ta tsoma baki kai tsaye a rikicin, yana mai cewa: “Duk wani yunkurin soja daga Amurka zai janyo barna mai tsanani da ba za a iya gyarawa ba.”
https://www.krmhausa.com/2025/06/harin-israila-kan-iran-barazana-ne-ga.html
A halin yanzu, dubban mutane na tsere daga birnin Tehran bayan harin sama da jiragen yakin Isra’ila suka kai a daren Laraba. Wata majiya daga Amurka ta bayyana cewa Shugaba Trump na duba yiwuwar shiga yakin don kai hare-hare tare da Isra’ila kan wuraren nukiliyar Iran.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta tura jiragen yaki guda 50 da suka kai farmaki kan wurare kusan 20 a Tehran, ciki har da wuraren sarrafa kayan hada makamai masu guba da makaman roka.
https://www.krmhausa.com/2025/06/israila-na-yunkurun-faaa-hari-kan-iran.html
A wata sanarwa da jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya da ke Geneva, Ali Bahreini, ya fitar, ya bayyana cewa Iran ta riga ta sanar da Amurka cewa za ta rama duk wani harin kai tsaye da Amurka ta yi. Ya kuma zargi Amurka da hannu a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa.