Hadakar ‘yan adawa ta ƙasa, National Opposition Coalition Group, ta sanar da neman rijistar sabuwar jam’iyyar siyasa, mai suna All Democratic Alliance (ADA) a Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa (INEC).
Sabuwar jam’iyyar na samun goyon bayan manyan 'yan siyasa, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
An tura buƙatar neman rijistar a ranar 19 ga Yuni, kuma INEC ta tabbatar da karɓar buƙatar a ranar Juma’a.
Hadakar ta ce, kafa jam’iyyar ADA na da nufin ƙarfafa gwiwar ‘yan adawa domin fitar da Shugaba Bola Tinubu daga mulki a zaɓe na gaba.
Tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, da kuma Dr. Umar Ardo, wanda ya kafa League of Northern Democrats kuma tsohon hadimin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, su na daga cikin masu mara wa wannan sabuwar tafiyar baya.
Takardar buƙatar da aka aikewa INEC na dauke da sanya hannun Shugaban riko na jam’iyyar, Chief Akin A. Rickets, da kuma Sakataren riko na ƙasa, Abdullahi Elayo.
Sashe na takardar ya bayyana cewa:
“Muna neman izinin Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa domin rijistar ƙungiyarmu mai suna All Democratic Alliance (ADA) a matsayin jam’iyyar siyasa. Wannan ya biyo bayan shawarar da National Coalition Group ta yanke na neman cikakken rijista a matsayin jam'iyyar siyasa.”
Idan aka amince da wannan buƙata, ADA za ta zama sabuwar jam’iyyar siyasa mai cike da manyan sunaye a fagen siyasar Najeriya, tare da tsayawa takara a babban zaɓen 2027