A wani bangare na tsaftace abubuwan da al'umma ke amfani da su, hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) ta rufe wuraren hada ruwa da na maganin gargajiya da gidan Burodi, a Jihar Kaduna.
Shugaban hukumar NAFDAC a Jihar Kaduna na jihar, Nasiru Mato, wanda ya jagoranci tawagar, ya bayyana cewa wasu daga cikin wuraren da aka rufe ba su da rajista da hukumar, yayin da wasu kuma suka gaza cika ƙa'idodin da ake buƙata domin gudanar da irin waɗannan sana'o'i.
Mato, ya ce hukumar ta rufe waɗannan wuraren ne saboda sun gaza cika ka’idojin buɗe masana’antu. Kana suna aiki ba tare da lasisi daga NAFDAC ba. Kana kuma, wuraren ba su da tsafta ko kaɗan,”Ya kara da cewa akwai damuwa game da yadda wasu ke amfani da lambar NAFDAC ba bisa ƙa’ida ba domin buga su a jikin kayayyakinsu.
Nasiru Mato, ya kara da cewa ganin kayayyaki da lambar NAFDAC ba yana nufin an yi rijista da hukumar ba ne. Wasu na kirkirar lambobin ne da kansu. Irin waɗannan kayayyaki ba su da sahihancin amincewar NAFDAC.
Mato ya ce samar da maganin gargajiya mai suna AJI GARAU, wanda aka tarar ana hada hadar su a lokacin ziyarar, ya karya duk ƙa’idodin tsafta, sannan kuma ma’aikata da hanyoyin samarwa bai dace da inganci da lafiyar amfani da magani ba. Ya ce Dukkan kayan aikin da ake amfani da su, da kayayyakin da aka kammala, ba su da amincewa kuma ba su da sahihanci ko bayanan da suka dace,” .
NAFDAC ta kwace kayayyakin don ci gaba da bincike, yayin da ta rufe wuraren a matsayin hukuncin farko. Mato ya kuma jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da farautar masu karya dokar samar da kayayyaki a kowane ɓangare na jihar.