Rayuwa ta fara komawa daidai a ƙasar Qatar bayan shaf dare cike da fargaba da rashin tabbas, sakamakon harin da Iran ta kai kan sansanin sojin Amurka da ke ƙasar.
A daren Litinin, Iran ta harba makamai masu linzami guda 19 zuwa sansanin Al Udeid da ke da nisan kilomita 35 daga birnin Doha, babban birnin Qatar. Sai dai jami’ai a ma’aikatar Cikin gida sun tabbatar da cewa dakarun tsaron Qatar sun yi nasarar tare makamai 18 daga cikin su.
Harin ya haddasa firgici a birnin Doha, inda aka ga makamai na ketawa ta sararin samaniyar birnin yayin da mazauna suka shiga cikin matsanancin tashin hankali.
ƙasashen Amurka da Birtaniya sun shawarci 'yan ƙasarsu da su zauna a gida don kauce wa shiga haɗari.
A matsayin wani shiri na matakin kariya, Qatar ta rufe sararin samaniyarta tare da sanar da dakatar da zuwa makaranta a ranar Talata. Haka kuma, mutane da dama an ba su shawarar su yi aiki daga gida.
Sai dai bayan awanni 12 da faruwar harin, an ga komai na komawa daidai a birnin Doha. Tituna sun cika da ababen hawa, yayin da al'umma ke cigaba da gudanar da rayuwarsu cikin natsuwa kamar yadda aka saba, duk da firgicin da suka fuskanta a daren jiya.