Akalla Falasɗinawa 35 ne suka rasa rayukansu a zirin Gazza sakamakon harbe-harbe da sojojin Isra’ila suka kai, inda mafi yawan wadanda aka kashe ke kusa da wurin raba kayayyakin agaji da Gidauniyar Agajin Gazza (GHF) ke gudanarwa, wadda Amurka ke marawa baya, in ji hukumomin lafiya na cikin gida.
Likitoci a asibitocin Al-Awda da Al-Aqsa da ke tsakiyar Gazza, inda aka kai galibin gawarwaki da wadanda suka jikkata, sun bayyana cewa akalla mutane 15 ne suka mutu yayin da suke kokarin isa wurin rabon kayan agaji na GHF da ke kusa da hanyar Netzarim.Sauran wadanda suka mutu kuma an ce sun rasu ne a wasu hare-hare daban-daban da aka kai a sassan Gazza.
Sojojin Isra’ila da kuma GHF ba su fitar da wata sanarwa kai tsaye kan lamarin da ya faru a ranar Asabar ba.
GHF ta fara raba kayan abinci a Gazza tun karshen watan Mayu, inda ta bullo da wata sabuwar hanya ta raba agaji.
Ma’aikatar Lafiya ta Gazza ta ce, tun lokacin da GHF ta fara aiki a Gaza, akalla mutane 274 ne aka kashe, yayin da wasu sama da 2,000 suka jikkata a wuraren da ake rabon agajin.
Hamas ta musanta zargin Isra’ila cewa tana sace kayayykin agajin, inda ta zargi Isra’ila da “yin amfani da yunwa a matsayin makamin yaƙi da kuma mayar da wuraren raba kayan agaji zuwa tarko hallaka fararen hula da dama.”
Dakarun Isra’ila sun umarci mazauna Khan Younis da garuruwan Abassan da Bani Suhaila da ke kudancin Gazza su bar gidajensu su nufi yammacin yankin zuwa wurin da ake kira “yankin jinƙai”, tare da jan kunnen cewa za su kai farmaki a kan “kungiyoyin ta’addanci” da ke yankin.
Yakin Gazza ya ɓarke ne kimanin watanni 20 da suka gabata bayan da mayaƙa suka kai hari a Isra’ila, inda suka kashe mutane 1,200 tare da yin garkuwa da mutane 251, a ranar 7 ga Oktoba, 2023 — wacce aka bayyana a matsayin rana mafi muni a tarihin Isra’ila.
A cewar hukumomin lafiya na Gazza, hare-haren da Isra’ila ke kaiwa ya kashe kusan Falasɗinawa 55,000 — yawancin su fararen hula ne — tare da rushe mafi yawan gine-gine a wannan wuri da ke da yawan jama’a fiye da miliyan biyu.
Yawancin al’ummar yankin na yin ƙaura, yayin da yunwa da rashin abinci suka yi musu katutu.
Ko da yake Amurka, Masar da Qatar na ci gaba da ƙoƙarin ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, amma babu wata alama da ke nuna cewa Isra’ila ko Hamas na da niyyar sassauta bukatunsu, inda kowanne bangare ke dora alhakin gazawar cimma matsaya a kan ɗayan.