Matasa Sun Gudanar Da Zanga-zanga Tare Da Toshe Hanyar Abuja Zuwa Makurdi

Wasu fusatattun matasan jihar Benue sun gudanar da zanga-zanga a ranar Lahadi, inda suka tare babbar hanyar Abuja zuwa Makurdi, suna nuna rashin jin daɗinsu kan ci gaba da kashe-kashe a jihar.

Zanga-zangar ta samu halartar matasa sanye da baƙaƙen kaya, dauke da ganyen dabino da alluna masu dauke da rubuce-rubuce daban-daban. Sun toshe hanyar da ake samun zirga-zirga, lamarin da ya janyo cunkoso da firgici ga matafiya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa masu zanga-zangar sun hana motocin wucewa, lamarin da ya haifar da cinkoso mai tsanani a hanyar.

Wannan zanga-zanga ta zo ne kasa da awanni 24 bayan wani hari da ake zargin makiyaya dauke da makamai suka kai wa al’ummar Yelewata da ke karamar hukumar Guma, inda aka ruwaito fiye da mutum 200 sun rasa rayukansu.

A baya-bayan nan, gwamnatin jihar Benue ta fitar da gargadi kan gudanar da taruka ko zanga-zangar da ba bisa ka’ida ba, musamman daga matasa, sakamakon hauhawar tarzoma a wasu sassan jihar.

Sai dai duk da wannan kira na zaman lafiya, matasan sun bayyana cewa sun ji kamar an yi watsi da su, suna kuma bukatar matakan tsaro na gaskiya da kuma adalci ga wadanda suka rasa rayukansu.

Previous Post Next Post