Iyalan wadanda abin ya shafa na ci gaba da jiran sabbin labarai a ranar Asabar, bayan daya daga cikin mafi munin hadurran jirgin sama da aka samu a ‘yan shekarun nan, inda adadin wadanda suka mutu ya kai mutane 279.
Jirgin fasinja na Air India kirar Boeing 787-8 Dreamliner ya nemi daukin gaggawa kafin ya fadi a ranar Alhamis, inda ya taba gine-ginen jama'a a birnin Ahmedabad, dake arewacin Indiya.
A ranar Asabar, wata majiya daga ‘yan sanda ta tabbatar da cewa an gano gawarwaki 279 daga wurin da hatsarin ya faru – wanda ke zama daya daga cikin mafi muni da aka gani a karni na 21.
An samu mutum daya kacal da ya tsira daga cikin fasinjoji da ma’aikatan jirgi 242 da ya fadi. jirgin ya fada cikin wani gidan kwanan ma’aikatan lafiya.
Aƙalla mutane 38 daga cikin mazauna yankin da jirgin ya fadi suka mutu.
Ana ci gaba da daukar samfurin kwayar halittar DNA'yan uwan Mamatan a Ahmedabad don taimaka wajen tantance gawarwakin.
Ba za a tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ba har s sai an kammala gwaje-gwajen DNA .
Kamfanin Air India ya bayyana cewa jirgin ya dauki fassinjoji 169 ‘yan Indiya, 53 ‘yan Birtaniya, bakwai ‘yan Portugal, da dan kasar Kanada, tare da ma’aikatan jirgi guda 12.
https://www.krmhausa.com/2025/06/narendra-modi-ya-nuna-alhini-kan.html
Wadanda suka rasa rayukansu sun hada da wani shahararren dan siyasa har da wani matashi mai sayar da shayi.
Wanda ya tsira kadai, Vishwash Kumar Ramesh, mai shekaru 40 da haihuwa, ya ce har yanzu ba zai iya bayani yadda ya tsira ba.
“Da farko na dauka zan mutu, amma na bude idona na ga har yanzu ina raye,” in ji Ramesh, dan asalin Birtaniya, in ji Vishwash Kumar Ramesh
Ministan harkokin sufurin jiragen sama, Ram Mohan Naidu Kinjarapu, ya bayyana a ranar Juma’a cewa an gano na’urar daukar bayanan jirgi (black box) kuma hakan zai taimaka sosai wajen bincike.
Kungiyar masu bincike na forensics na ci gaba da neman na’urar black box ta biyu, don gano dalilin da yasa jirgin ya fadi bayan ya tashi sama da kusan tsawon mita 100 kacal.
Kamfanin Boeing na Amurka ya ce yana tuntubar Kamfanin Air India kuma yana nan a shirye don bayar da goyon baya, inda wata majiya ta ce wannan shi ne karo na farko da irin wannan jirgi na Dreamliner ya fuskanci irin wannan tsanani.