Sarkin Jordan, Abdullah II, ya bayyana cewa sabon bshirin faɗaɗa harin da Isra’ila ke kai wa Iran babban barazana ne ga kowa da ma duniya. Ya bayyana haka ne yayin jawabi ga Majalisar Tarayyar Turai a Strasbourg ranar Talata.
Ya ce “Ba za a iya hango inda wannan yakin zai tsaya ba… hare-haren da Isra’ila ke kai wa Iran na iya haifar da mummunan rikici da zai shafi yankin da ma duniya baki ɗaya,”.
Sarkin ya ci gaba da cewa idan duniya ta kasa ɗaukar mataki mai ƙarfi, hakan na nufin an amince da sauya ma’anar tunanin ɗan adam. Ya bayyana takaicinsa kan yadda Isra’ila ke ci gaba da rushe gidajen Falasdinawa, da sare itatuwan zaitun da lalata ababen more rayuwa.
Abdullahi II ya ce “Idan waɗannan abubuwa suka ci gaba, to tabbas za su rusa tushen hali na gari da imani da 'yancin ɗan adam,”.
Sarki Abdullah ya sake jaddada bukatar ƙirƙirar ƙasar Falasɗinu mai cikakken ‘yanci da ikon mulki tare da bai wa al’ummar Falasɗinu ‘yancin rayuwa da tafiyar da rayuwarsu.
“Ba za a iya samun zaman lafiya a duniya ba, har sai duniya ta tashi tsaye wajen kawo ƙarshen yaƙin Ukraine da kuma rikicin Falasɗinu da Isra’ila wanda ya fi kowanne rikici daukar tsawon lokaci da mummunan tasiri,” a cewarsa.
Ya soki gazawar dokokin kasa da kasa da ƙungiyoyin duniya wajen dakile rashin imanin da ke faruwa a Gaza, inda ya ce abubuwan da a baya ake ɗauka a matsayin kisan kare dangi yanzu sun zama ruwan dare.
Ya kara da cewa “Yadda ake amfani da yunwa a matsayin makami, da kuma kai hari kan likitoci, ‘yan jarida da yara, duk sun zama ruwan dare saboda shiru da gazawar duniya,”.
Sarkin ya ja hankalin shugabannin Turai da su taka rawar gani wajen zabar hanyar da ta dace. Ya kuma tabbatar da cewa Jordan za ta ci gaba da mara wa Tarayyar Turai baya.
“Dole ne a kawo karshen wannan rikici, kuma mafita tana cikin bin dokokin duniya. Tsohuwar hanya ce amma za a iya komawa gare ta idan har mun yi shiri da kuma bada haɗin kai,”.