Majalisar Dokokin Jihar Yobe ta shirya gudanar da zaman jin ra'ayin al'umma a matakin yanki kan kudirin doka da ke neman tilasta duk masu shirin yin aure su yi gwajin jinin kwayar halittar jini [genotype] da cutar hanta [hepatitis] a fadin jihar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Kwamitin wucin gadi kan kudirin, Hon. Kachalla Ajiya Maina, ya fitar kuma ya rabawa manema labarai a Damaturu.
A cewar sanarwar, zaman farko na jin ra’ayin al'umma zai gudana ne a ranar Alhamis, 19 ga Yuni, 2025, ga jama'ar yankin Sanatan Yobe ta Arewa, wanda za a gudanar a Kwalejin Ilimi ta Umar Suleiman da ke Gashua da misalin ƙarfe 11:00 na safe.
Sai kuma taron da za a gudanar a yankin Sanatan Yobe ta Kudu, da za a gudanar da zaman a ranar Litinin, 23 ga Yuni, 2025, a Kwalejin koyon harkokin gudanarwa da Fasahar Mulki da ke Potiskum, da ƙarfe 11:00 na safe.
Yankin Sanatan Yobe ta Gabas kuma zai karɓi bakuncin zaman a ranar Laraba, 25 ga Yuni, a Kwalejin Koyon Aikin Jinya da Ungozoma ta Shehu Sule da ke Damaturu, tun daga ƙarfe 11:00 na safe.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Rt. Hon. Chiroma Buba Mashio, shi ne babban bako na musamman a dukkanin zaman.
Ana sa ran halartar sarakunan gargajiya, dagatai da hakimai, shugabannin addinai, shugabannin kananan hukumomi, kungiyoyin farar hula da sauran jama’a don bayar da gudummawar ra’ayoyi da shawarwari domin cimma nasarar wannan kudiri a duk matakan da suka dace.