Isra’ila Na Yunkurun Faɗaɗa Hari Kan Iran

Isra’ila ta bukaci  dubban mutane da su fice daga tsakiyar birnin Tehran, yayin da hare-harenta kan Iran ke ƙaruwa a rana ta biyar da fara rikici tsakanin kasashen.



A cewar Isra’ila, an kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliya na Iran, masana’antar makaman ballistic, da kuma shugabannin sojin Iran, a wani yunkuri na dakile Iran daga samar da makamin nukiliya.

Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa:

“Za mu ci gaba da wannan aiki har sai mun kawo karshen barazanar Iran gaba ɗaya, wadda ta ke haifar da firgici ga zaman lafiyar Isra’ila.”

Iran ta mayar da martani da hare-hare kan birnin Tel Aviv. Wasu daga cikin makaman da ta harba basu kai ga inda aika su ba, wasu kuma sun faɗa kan gine-gine a Isra’ila.

Rahotanni daga ma’aikatar lafiya a Iran sun nuna cewa mutane 1,277 sun jikkata,

Tasirin Rikicin ga Duniya

Sabon rikicin ya tilasta ƙasashen Gabas ta Tsakiya da dama, ciki har da Iraq, Jordan da Lebanon, rufe sararin samaniyarsu ga jiragen sama. Wannan ya sa tashoshin jiragen sama da dama sun dakatar da zirga-zirga, lamarin da ya bar dubban fasinjoji a cikin halin damuwa – kana ba halin komawa gida.

Previous Post Next Post