Yarima Mohammed bin Salman Ya Jaddada Bukatar Daukar Matakin Kasa da Kasa Kan Hare-haren Isra'ila a Gaza

Yarima, Mohammed bin Salman, ya sake jaddada muhimmancin rawar da al’ummar duniya za su taka wajen kawo karshen mummunan tasirin “harin Isra’ila” a Gaza.

Yayin wani jawabi ga baki da jami’an gwamnati a lokacin bikin babbar Sallah  a Mina, wanda kamfanin dillancin labarai na Saudiyya (SPA) ya ruwaito, Yarima Mohammed bin Salman ya bayyana cewa:
"Wahalhalun da 'yan’uwanmu na Palastinu ke fuskanta na ci gaba sakamakon harin Isra’ila da ke kaiwa a yankin."

Ya kara da cewa:
"Muna sake jaddada muhimmancin rawar da al’ummar duniya ke da ita wajen kawo karshen mummunan tasirin wannan hari da kare fararen hula da basu ji ba, basu gani ba, da kuma neman samar da sabon yanayi da zai ba Palastinu damar samun zaman lafiya bisa doka ta kasa da kasa da kudurorin da suka dace."

Yarima ya bayyana haka ne yayin ganawa daal'umma a fadarsa da ke Mina.

Har ila yau, ya bayyana yadda Allah ya girmama kasar Saudiyya da hidimtawa Masallatai Masu Alfarma da maziyartansu, ciki har da mahajjata da masu yin Umrah da sauran baki.
Ya ce "Mun sanya wannan hidima a gaba cikin ayyukanmu, kuma muna amfani da duk wata dama da muke da ita domin tabbatar da cewa bakin Allah sun gudanar da ibadarsu cikin sauki da kwanciyar hankali," 

Yariman ya kara jaddada cewa Saudiyya na  himma wajen cika wannan nauyi, yana mai bayyana cewa wannan aiki babban girmamawa ne da amana  mai nauyi.

A karshe ya ce:
"Muna rokon Allah Madaukaki da ya dawwamar da tsaro da zaman lafiya a kasarmu da  dukkan kasashen Musulmi da kuma duniya baki daya."
"Allah Ya karbi aikin Hajjin mahajjata kuma ya koma  da su  ga iyalansu lafiya."

Previous Post Next Post