‘Yan Sandan a Jihar Filato sun kama mutane 22 da ake zargi da hannu a kisan wasu fasinjoji takwas da aka kashe a yankin Mangun, cikin karamar hukumar Mangu ta jihar.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Alfred Alabo, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Emmanuel O. Adesina, tare da shugabannin sauran hukumomin tsaro, sun kai ziyara zuwa wurin da lamarin ya faru tun da safiyar Asabar domin tantance halin da ake ciki da kuma daukar matakan hana sake faruwar hakan.
Ya ce “Rundunar ta kama mutane 22 da ake zargi da hannu a harin. Kwamishinan ‘yan sanda ya tura jami’an sashen leken asiri na jihar (SID) zuwa Mangu domin tattara sahihan bayanai."
Ya kara da cewa an kuma tura jami’an sashen bincike na musamman (CID) domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin. kazalika, kwamishinan ya aika da tawagogin kwararrun jami’ai da kayan aiki na musamman zuwa yankin don taimaka wa binciken da kuma cafke sauran da suka tsere.
DSP Alabo ya ce:
“Kwamishinan 'yan sanda na jihar Filato yana tabbatar wa da al’ummar jihar cewa rundunar zata tabbatar an kama duk wanda ke da hannu domin ganin an gurfanar don girbar sakamakon danyen aiki.”
Ya kuma bukaci al’ummar jihar, musamman matasa, da su kauce wa daukar doka a hannunsu tare da kai rahoton duk wani motsi ko zargi da suke da shi zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko wata hukuma ta tsaro.
