Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Yankin Afirka da Gidauniyar TY Danjuma sun rattaba hannu kan yarjejeniya dala miliyan $2.26 domin karfafa tsarin kiwon lafiya a Najeriya cikin shekaru goma masu zuwa.
An gudanar da bikin rattaba hannu ranar Litinin a Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja, inda manyan masu ruwa da tsaki suka halarta, ciki har da wakilan Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a ta Tarayya, jami’an jihohin da suka hada da Taraba, Enugu da Edo, da maa membobin diflomasiyya.
Yarjejeniyar na da nufin inganta damar samun muhimman aiyukan lafiya, musamman a al’ummomin da ke fama da karancin aiyuka, inganta lafiyar Mata da Yara, da gina tsarin daukar matsalolin gaggawa na lafiya tare da daidaitawa su da manufofin ci gaba mai dorewa na Duniya (SDGs).
Da yake jawabi yayin bikin, Mukaddashin Daraktan Yankin Afirka na WHO, Chikwe Ihekweazu, ya bayyana wannan hadin gwiwa a matsayin muhimmin mataki wajen amfani da tallafi daga ‘yan Afirka domin tinkarar kalubalen kiwon lafiya da ke addabar yankin.
Mista Ihekweazu ya bayyana cewa kudin tallafin zai baiwa WHO sassauci wajen aiwatar da tsarin aikinta har zuwa watan Disamba 2034. Yana mai cewa wannan gudunmawa ta zo a daidai lokacin da ake bukatarta.
Ya ce “Ko da yake muna fuskantar kalubale, mu ‘yan Afirka za mu jagoranci kanmu. za mu fuskanci matsalolinmu da kanmu kuma mu ci gaba da tafiya.”
Ya kara da cewa wannan tallafi zai baiwa WHO a Nigeria damar daidaita bukatun lafiyar da ke tasowa da inganta tsarin kiwon lafiya na kasa, musamman a bangaren kula da lafiyar Mata da yara. “Wannan shiri ya tsarin WHO don karfafa samun kudaden don dorewar kiwon lafiya a nahiyar Afirka.”
A jawabin maraba, Wakilin WHO a Najeriya, Walter Mulombo, ya bayyana mahimmancin hadin gwiwar, yana mai cewa wannan wani misali ne na hadin gwiwar da ke gudana a cikin gida domin tallafa wa lafiya.
Mista Mulombo ya nuna cewa wannan hadin gwiwa ya zo ne a lokaci da kasashe ke fuskantar kiraye-kiraye na kara daukar nauyin lafiyar jama’arsu da kokarin samar da kudade. “Wannan yana da nasaba da muradun lafiyar kasa da kuma manufofin ci gaba mai dorewa. Hadin gwiwar da ya dace da manufofin Hadin gwiwar da WHO karo na hudu (CCSIV)
A yayin taron, Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Muhammad Pate, ya yaba da wannan shiri, yana mai cewa yana da nasaba da shirin farfado da cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko (PHC) karkashin Shirin sabunta fata (Renewed Hope Investment Initiative) na Shugaba Bola Tinubu.
Mista Pate, wanda Daraktan Lafiyar Jama’a, Godwin Ntadom, ya wakilta, ya bayyana cewa Najeriya na da niyyar fadada tsarin Asibitoci a matakin farko PHC ta hanyar karfafa ma’aikata, sabunta gine-gine da samar da wadataccen kudi ta hanyar Asusun Tallafa wa Kiwon Lafiya (BHCPF).
A nasa bangaren Shugaban kuma wanda ya samar da Gidauniyar TY Danjuma, Theophilus Danjuma, ya bayyana cewa gidauniyar na alfahari da hadin gwiwar da WHO domin inganta lafiyar 'yan Najeriya.
Mista Danjuma ya bayyana cewa shirin zai mayar da hankali wajen fadada damar samun aiyukan lafiya Mata da yara da al’ummomin da suka fi bukata a jihohin Taraba, Edo da Enugu.
Ya kara da cewa Tun daga kafuwarta a shekarar 2009, Gidauniyar TY Danjuma na tallafa wa kungiyoyin gida wajen aiwatar da shirye-shiryen ci gaban bangaren lafiya.