Hukumar shirya jarabawa ta Ƙasa (NECO) ta bayyana cewa ta shirya gudanar da jarabawar SSCE na watan Nuwamba da Disamba ga ɗalibai masu zaman kansu.
Shugaban hukumar ta NECO, Farfesa Dantani Wushishi, shine ya bayyana hakan, inda ya jaddada muhimmancin wayar da kai domin jawo hankalin masu ruwa da tsaki kan wannan sabon tsarin gudanar da jarabawar SSCE.
Ya ce NECO na ci gaba da gudanar dashirin wayar da kai ta hanyar tarurruka da jama’a da masu ruwa da tsaki a fadin jihohi Kasar nan.
Tags:
ilimi