Mai horasa da Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Eric Chelle ya nuna damuwarsa kan yadda kungiyar ta gudanar da wasan karshe a gasar cin kofin Unity na 2025.
Yayin da yake bayyana irin nasarorin da aka samu a gasar, Chelle ya jaddada cewa dole ne tawagar yan wasan na najeriya su kara jajircewa don samun gurbin buga gasar kofin duniya na shekarar 2026 daze wakana a kasar Amurka.
Mai horasawar ya bayyana gasar Unity Cup a matsayin kofinsa na farko bayan zama mai horaswar super eagle duk da a baya ya lashe wasu kofunan da dama a matsayinsa na dan wasa.
A hannu guda kuma, dan wasan gaba na kkk ta PSG, Ousmane Dembele, ya zama gwarzon dan wasan gasar zakarun nahiyar turai a kakar wasa ta bana.
PSG ta lashe kofin a karon farko bayan da ta lallasa Inter Milan da ci 5-0 ranar Asabar a filin wasa na Alianz Arena dake birin Munich a kasar Jamus, duk da cewa Dembele bai samu nasarar zura kwallo a raga ba, ya taimaka wajen zura kwallaye biyu.