Hukumar Tsaro Ta Civil Defence, Ta Bayar Da Umarnin Gaggawar Kara Matakan Tsaro A Fadin Kasar Domin Kare Muhimman Kadarorin Kasa Da Tabbatar Da Doka da Oda.

Shugaban Hukumar tsaro ta civil defence, Dr. Ahmed Audi, ya bayar da umarnin gaggawa na kara matakan tsaro a fadin kasar domin kare muhimman kadarorin kasa da tabbatar da doka da oda.

A cewar hukumar, bayanan leken asiri da suka samu sun nuna yiwuwar gudanar da zanga-zangar lumana a jihohi da dama a yau, ciki har da Babban Birnin Tarayya, Legas, Ondo, Oyo, Delta da Rivers da sauransu.

A cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun hukumar, Afolabi Babawale, ya fitar, Audi ya umurci jami’an hukumar da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana a duk wuraren da aka gano a matsayin wuraren da zanga-zanga ka iya gudana, cibiyoyin nishadi, da sauran wuraren taruwar jama’a.

Haka kuma, ya yi gargaɗi mai tsanani ga matasa da kada su bari a yi amfani da su wajen aikata laifuka, yana mai cewa duk wanda aka kama yana ƙoƙarin tayar da rikici ko lalata dukiya, za a kama shi kuma a gurfanar da shi gaban kuliya.


Previous Post Next Post