Jami’an tsaro sun toshe babban kofar shiga majalisar dokokin kasa da ke Abuja da safiyar yau domin hana masu zanga-zanga shiga harabar majalisar.
Jami’an da aka girke sun hada da na civil defence da kuma ‘yan sanda dauke da makamai da ke tsare kofar shiga majalisar.
Zanga-zangar, wadda kungiyoyin Take It Back Movement da wasu kungiyoyin fararen hula suka shirya, na da nufin jaddada abin da suka bayyana a matsayin “shekaru biyu na mulkin danniya da wahala” a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Masu shirya zanga-zangar sun mayar da ita zuwa majalisar dokokin kasa, inda ake sa ran Shugaba Tinubu zai yi jawabi a zaman hadin gwiwa na majalisar a wani bangare na bukukuwan ranar Dimokuradiyya.
Tags:
Labarai