Shugaban Hukumar UNESCO Read and Earn Federation, Abdulsalami Ladigbolu-Oranmiyan, ya yi kira da a dauki mataki a kasa da ma duniya baki daya don kawo karshen aikatau da yara ke yi.
Ladigbolu-Oranmiyan, wanda ya bayyana hakan, ya jaddada cewa aikatau da yara ke yi na ci gaba da hana miliyoyin yara a Najeriya da duniya damar samun ilimi, tsaro, da makoma mai kyau.
Ya gargadi cewa ci gaba da wanzuwar aikatau na yara na hana cimma manufofin cigaban Najeriya da kuma alkawarin duniya na cimma manufofin cigaban dorewa na Majalisar Dinkin Duniya, musamman SDG 8.7, wanda ke nufin kawar da dukkan nau’o’in aikatau na yara.
Ya kuma bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya kara zage dantse a karkashin tsarin Renewed Hope ta hanyar daidaita manufofin kasa da tsarin Majalisar Dinkin Duniya na cigaba mai dorewa.