Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta bayyana cewa ta tura karin jiragen yaki zuwa yankin Arewa ta Tsakiya karkashin Operation Whirl Stroke (OPWS) domin karfafa kokarin tabbatar da zaman lafiya, musamman bayan kashe sama da mutane 100 a garin Yelewata da ke kan iyakar karamar hukumar Guma a jihar Benue.
Wannan mataki na zuwa ne bayan wani mummunan hari da wasu da ake zargin wasu dauke da makamai suka kai, wanda ya haddasa zanga-zanga ta tsawon kwanaki biyu a jihar.
A wani sa'ko da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Talata, Shugaban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Hasan Abubakar, shine ya bayyana hakan yayin wata ziyarar tantance ayyukan rundunar a shelkwatar Tactical Air Command da ke Makurdi, babban birnin jihar Benue.
A lokacin ziyarar, Air Marshal Abubakar ya gudanar da taro tare da manyan hafsoshin tsaro ciki har da Shugaban Sojin Kasa, Olufemi Oluyede, wakilin Shugaban rundunar Sojin Ruwa, Olusegun Ferreira, da sauran kwamandojin manyan rundunar. An bayar da rahotanni kan yadda hadin gwiwar jami’an tsaro ke ci gaba da gudanar da aiki a jihohin Benue, Nasarawa, da Taraba.
A cewarsa, karin jiragen da aka tura sun habaka tasirin aiki ta sama, suna bayar da cikakkun rahotanni da bada bayanai, kula da hare-hare daga sama, da kai farmaki da nufin ruguza sansanonin ‘yan ta’adda da maboyarsu.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi Allah wadai da harin da aka kai a Yelewata, inda ya umarci shugabannin tsaro da su hanzarta daukar matakin dawo da zaman lafiya.
Ya ce: “Matukar zaman lafiya na cikin barazana, dole mu dauki matakan da suka da ce.”
Air Marshal Abubakar ya jaddada cewa wadannan matakai na cikin kokarin gwamnatin tarayya na kawo karkashen kai hare-hare a yankin tsakiyar Kasar (Middle Belt) tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, har sai an samu cikakken zaman lafiya.