Hukumar dakile yaduwar cutuuka ta Kasa (NCDC) ta bayyana karuwar yawan mace-mace da aka samu sakamakon barkewar zazzabin Lassa a Kasar nan, yayin da cutar ke ci gaba da yaduwa a jihohi da dama.
A cewar rahoton, Najeriya ta samu jimillar mutune 143 da suka mutu daga cikin mutune 758 da aka tabbatar sun kamu da cutar Lassa tun farkon shekarar. Wannan ya nuna cewa kaso 18.9 cikin 100 na mutanen da suka kamu da cutar sun mutu – wanda ya dara kaso 17.8 cikin 100 da aka samu a makamancin wannan lokaci a shekarar 2024.
NCDC ta kuma bayyana cewa an samu sabbin mutune 11 da aka tabbatar sun kamu da cutar a wannan makon, sabanin mutune 8 da aka samu a makon da ya gabata. Sabbin wadanda suka kamu da cutar sun fito ne daga jihohin Ondo, Edo, Bauchi da Taraba.
"Kunshin rahoton ya nuna cewa a shekarar 2025, jihohi 18 ne aka samu aƙalla mutum guda da aka tabbatar ya kamu da cutar, da ta bazu a kananan hukumomi 96. Sai dai kaso 90 cikin 100 na daukacin wadanda suka kamu da cutar an gano su ne daga jihohi biyar, da suka hada da: Ondo (31%), Bauchi (25%), Edo (16%), Taraba (15%), da Ebonyi (3%),".
Rahoton ya kuma nuna cewa mafi yawan wadanda cutar ke kamawa matasa ne masu shekaru tsakanin 21 zuwa 30, inda aka bayyana matsakaicin shekarun wadanda suka kamu da cutar da 30. Haka kuma, an samu wani daga cikin ma’aikatan lafiya da ya kamu da cutar a wannan makon, wanda ya kai adadin ma’aikatan lafiya da suka kamu da cutar a bana zuwa 23.
Daga cikin kalubalen da ke kara haifar da yaduwar cutar sun hada da: jinkirin zuwa asibiti da halin rashin neman kulawar jami'an lafiya da wuri da tsadar magani, rashin tsafta da kuma karancin wayar da kai a cikin al’umma.
Don dakile yaduwar cutar da rage mace-mace, hukumar NCDC ta ce ta kafa kwamitin kula da hadurra daga bangarori da dama, tare da tura kungiyoyi na musamman guda 10 zuwa jihohin da cutar ta fi kamari.
Sauran matakan da aka dauka sun hada da: horar da ma’aikatan lafiya kan kula da masu dauke da cutar, kaddamar da dandalin koyar da dabarun kariya daga kamuwa da cutuka ta yanar gizo, fadakarwa a cikin al’umma, tsaftace muhalli, da kuma hada kai da kafafen yada labarai domin wayar da kan jama’a.
Hukumar ta bukaci ‘yan Najeriya da su kiyaye tsaftar muhalli da jikinsu, su nemi kulawar jami'an lafiya da wuri idan sun fuskanci alamomin cutar, tare da guje wa mu’amala da beraye, wadanda su ne manyan hanyoyin yaduwar cutar.
Zazzabin Lassa dai cuta ce mai hadari wadda kwayar cuta ke haddasawa, kuma tana yaduwa ta hanyar shakar tiririn fitsari ko bayan gidan berayen da ke dauke da cutar.