Jam'iyyar APC Ta 'Bara Kan Dalilin Rashin Kiran Sunan Mataimakin Shugaban Kasa, A Yayi Kadaddamar Da Takara

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, shiyyar Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu, ya bayyana dalilin da ya sa bai hada da sunan Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, a lokacin da ya bayyan a goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ba.



A wata zantawa da ya yi da gidan wani talabijin a  jiya, Salihu ya ce hakan ya yi daidai da tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar wanda ke bayyana cewa goyon baya a lokacin tsayawa takara ya shafi ‘yan takarar shugabanci ne kawai, ba tare da hadawa da abokan takararsu ba.

Ya ce wannan ne ya sa gwamnonin Yobe, Mai Mala Buni, da na Gombe, Inuwa Yahaya, suka bayyana goyon bayan su ga Tinubu ba tare da sun hada da Shettima ba, kodayake sun yaba masa a matsayin ɗan Arewa maso Gabas

Previous Post Next Post