Shugaban Falasdinu, Mahmud Abbas, ya bayyana cewa kungiyar Hamas dole ne ta mika makamanta, tare da kiran a tura dakarun kasa da kasa domin kare al’ummar Falasdinu, a cewar gwamnatin Faransa a ranar Talata.
A cikin wata wasika da ya aikawa Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman — wadanda za su jagoranci taron neman mafita kan tsarin kasashe biyu (two-state solution) — Abbas ya gabatar da matakan da ya ke ganin za su kawo karshen yaki a Gaza da kuma samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
Abbas ya ce “Hamas ba za ta ci gaba da mulkin Gaza ba kuma dole ne ta mika makamanta da kayan yaki ga Hukumar Tsaron Falasdinu,”.
Ya kara da cewa yana “shirye-shiryen gayyatar dakarun Larabawa da na kasa da kasa a karkashin izinin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya domin gudanar da aikin kare lafiya.”
Taron da za a gudanar a shelkwatar Majalisar Dinkin Duniya, nan gaba a wannan wata, zai duba yiwuwar dawo da tsarin kasashe biyu — inda Isra’ila ke da iko kan manyan sassan yankunan Falasdinu.
“Muna shirye mu kammala yarjejeniyar zaman lafiya, karkashin kulawa da goyon bayan kasa da kasa, domin kawo karshen mamayar Isra’ila da warware dukkan matsalolin da ke gabanmu,” in ji Abbas.
Shugaban na Falasdinu ya kuma nemi kungiyar Hamas ta “saki dukkan fursunoni da wadanda ta kama.”
Fadar Shugaban Faransa (Elysee Palace) ta bayyana matakan Abbas a matsayin “alkawura masu kyau da ba a taba gani ba, wanda ke nuna sahihancin kudurin neman aiwatar da mafita ta tsarin kasashe biyu.”
Shugaba Macron ya sha alwashin cewa zai amince da kafa kasar Falasdinu, amma ya bayyana wasu sharudda da suka hada da “kawo karshen daukar makamin Hamas.”
Abbas ya sake jaddada aniyarsa ta gyara hukumar Falasdinu da kuma gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisa cikin shekara guda karkashin kulawar kasa da kasa.
“Kasarmu ta Falasdinu ce kawai za ta rike aikin tsaro a yankinta, kuma ba mu da niyyar daukar makaman yaki,” in ji Abbas.