A wani mummunan farmaki da ke kara fitar da sabbin lamara a rikicin Gabas ta Tsakiya, Isra’ila ta kai hari kai tsaye kan babban birnin Iran da safiyar ranar Juma’a. Harin ya shafi wurare da dama ciki har da cibiyoyin sarrafa makaman nukiliya, wanda hakan ke nuni da yiwuwar barkewar yaki tsakanin manyan abokan gaba guda biyu na yankin.
Rahotanni sun nuna fitar hayaki daga cibiyar habaka makamashin nukiliya da ke Natanz — daya daga cikin muhimman wuraren da Iran ke gudanar da ayyukanta na nukiliya. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da rahoton gidan talabijin na Iran ya tabbatar da mutuwar babban kwamandan sojoji na Revolutionary Guard, Janar Hossein Salami. Hakanan wasu manyan jami’ai biyu da masana kimiyyar nukiliya biyu na daga cikin wadanda ake zargin sun mutu.Wannan hari — mafi girma da Iran ta fuskanta tun yakin Iran da Iraki a shekarun 1980 — na zuwa ne yayin da duniya ke cikin damuwa kan cigaban shirye-shiryen Iran na nukiliya. Isra’ila ta bayyana harin a matsayin matakin kare kai daga barazanar da ta ce Iran na shirin kera nukiliya.
Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce:
“Wannan barazana ce kai tsaye ga rayuwar kasar Isra’ila. Ko da wata guda ne ya rage, ko watanni kadan, ba za mu jira har Iran ta kammala makamin ba.”
A wani karin bayani, Netanyahu ya ce an kai harin ne kan cibiyoyin soja da na nukiliya, da kuma kan shugabannin cibiyoyin makamai masu linzami na Iran.
https://www.krmhausa.com/2025/06/yawan-falasdinawa-da-suka-mutu-yakin.html
A birnin Washington, gwamnatin Amurka karkashin shugabancin Trump ta nesanta kanta daga harin tare da gargaɗin kada a maida martani da zai shafi jami’a ko kadarorin Amurka.
Harin na Isra’ila na iya samun karbuwa a cikin gida, inda jama’a ke kallon Iran a matsayin babban barazana. Har ma shugaban ‘yan adawa Yair Lapid — duk da adawarsa da Netanyahu — ya goyi bayan matakin. Duk da haka, idan Iran ta mayar da martani da ya janyo asarar rayuka ko dakile harkokin yau da kullum a Isra’ila, ra’ayin jama’a na iya canjawa da gaggawa.
Rahotanni sun bayyana cewa jiragen yakin Isra’ila sun yi amfani da na’urorin tanka mai na sama da suka dade ana amfani da su don kai farmakin, wanda ya sa ana tantama ko jiragen sun shiga sararin samaniyar Iran ko dai sun harba makamai ne daga wani yanki dabam — watakila daga saman kasar Iraki, inda mutane suka ruwaito jin karar jiragen yaki a lokacin harin.Tuni dai wasu na ganin yiwuwar hakan, inda alamun kai hari suka fara bayyana tun makonni da suka gabata.