Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya bayyana bakin cikin sa kan hatsarin jirgin saman da ya faru a birnin Ahmedabad.
Rahotannin Krm Hausa sun kawo labarin wani jirgin sama mallakin Air India kirar Boeing 787, wanda ke kan hanyarsa daga Ahmedabad zuwa filin jirgin saman Gatwick na birnin London, ya yi hatsari a ranar Alhamis.
Jirgin mai lamba Flight 171 ya fadi jim kadan bayan tashinsa, inda majiyoyin ‘yan sanda suka ce yana dauke da fasinjoji da ma’aikata kimanin 242. Bincike ya nuna cewa jirgin ya mike sama tsayin kafa 625 tare da gudun kilomita 174 a cikin daƙiƙa guda kafin faduwarsa. Bidiyo daga wurin hadarin sun nuna hayaki na tashi daga nesa.
Modi ya ce “Hatsarin da ya faru a Ahmedabad ya girgiza mu kuma ya tayar mana da hankali. Lamarin na matukar tada hankali fiye da yadda za a iya bayyana shi da baki,”.
Firaministan ya kara da cewa yana ci gaba da tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa, ciki har da ministoci, domin ganin an tallafa wa wadanda lamarin ya shafa.
