Khamenei Ya Gargaɗi Isra’ila da Cewa Za Ta Fuskanci Mummunan Martani

Shugaban addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya fitar da wani gargaɗi mai tsanani ga Isra’ila, yana cewa ƙasar za ta fuskanci “martani mai raɗaɗi da azaba” bayan da ta kai wasu munanan hare-hare a muhimman wurare a Iran, ciki har da Tehran da kuma cibiyoyin makamashin nukiliya.


A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Khamenei ya bayyana cewa:

“Da wannan aika-aika, Isra'ila ta tsokano wa kanta ƙaddara mai raɗaɗi da ciwo, kuma tabbas za ta fuskanci sakamakon abinda ta shirya.”

Wannan kalamai na Khamenei na zuwa ne a daidai lokacin da ake fargabar rikici zai faɗaɗa tsakanin manyan abokan gaba biyu na Gabas ta Tsakiya, Isra’ila da Iran.

Previous Post Next Post