Gwamnatin Isra’ila ta sanar da rufe dukkan ofisoshin jakadancenta na kasashen waje na ɗan lokaci, bayan harin da ta kai kan Iran da safiyar Juma’a. Ma’aikatar Harkokin Waje ta Isra’ila ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
Sanarwar ta bayyana cewa saboda wannan mataki, ba za a iya samun jami'an diflomasiyyar Isra’ila da ke ƙasashen waje ba. Haka kuma, an bukaci ‘yan Isra’ila da ke waje da su cika wani fom na yanar gizo domin sabunta bayanan wurin da suke da kuma halin da suke ciki.
Ma’aikatar ta kuma gargadi ‘yan ƙasar da ke waje da su guji sanya alamu ko tambarin Isra’ila a bainar jama’a, da kaucewa wallafa bayanan da za su iya bayyana inda suke ko shirye-shiryensu na tafiye-tafiye a kafafen sada zumunta. Haka nan an shawarce su da su guji halartar taruka da ke da alaƙa da Isra’ila.Wannan mataki na biyo bayan harin da Isra’ila ta kai kan Iran ne, inda ta kai farmaki kan muhimman sansanonin soja da cibiyoyin nukiliya.
Rahotanni daga Iran sun ce harin ya hallaka manyan hafsoshin soja, ciki har da Shugaban Dakarun sojin kasar, Janar Mohammad Bagheri, da Kwamandan Rundunar IRGC, Hossein Salami.
A martaninsa, Jagoran Ƙasa na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi alwashin ramuwar gayya, inda ya ce “Isra’ila ta jefa kanta cikin hali na da na sani mai raɗaɗi.”