Sojoji Sun Kama Ɗan Kasar China da Wasu Bisa Zargin Taimaka wa ‘Yan Ta’adda a Borno

Dakarun Operation Hadin Kai sun cafke wasu mutane da ake zargi da taimaka wa ayyukan ta’addanci a jihar Borno, ciki har da wani ɗan ƙasar China.

Kakakin Shelkwatar Tsaro ta Ƙasa, Markus Kangye, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Juma’a, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.

Mr. Kangye ya ce an kama ɗan ƙasar China da ya bayyana kansa a matsayin mai tonan ma’adinai a wani samame da aka  kai a yankunan kananan hukumomin Kukawa da Ngala.

Ya kara da cewa “Yanzu haka, ana tsare da ɗan ƙasar ta China kuma ana ci gaba da yi masa tambayoyi,”.

Ya ƙara da cewa: “Bayan kammala bincike  za mu bayyana wa jama’a cikakkun bayanai game da dalilin da ya kai shi yankin, yadda aka kama shi, ko shi kaɗai ne ko kuma yana da abokan haɗin guiwa.”

Haka kuma, Mr. Kangye ya bayyana cewa daga ranar 6 zuwa 11 ga watan Yuni, mayakan Boko Haram da ISWAP da suka haɗa da maza, mata da yara da dama sun mika wuya.

Ya jaddada cewa rundunar sojin Najeriya za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da bin doka da oda, 

“Za mu ci gaba  da sanar da jama’a ci gaban da ake samu a kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ƙasarmu mai albarka,” in ji Kangye.

Previous Post Next Post