Sojoji Sun Lalata Haramtattun Matatun Man Fetur 21 a Yankin Neja Delta, Tare Da Kama Barayin Mai 23

Shelkwatar Tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun Operation Delta Safe sun gano tare da lalata haramtattun matatun  mai guda 21 a cikin mako guda a yankin Neja Delta, kuma an kama mutane 23 da ake zargi da satar mai.

Daraktan yaɗa Labaran na shelkwatar tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ranar Juma’a, inda ya bayyana irin nasarorin da dakarun suka samu a cikin makon da ya gabata.

Kangye ya ce dakarun na ci gaba da matsa kaimi wajen yakar barayin mai da sauran ‘yan ta’adda a yankin Neja Delta. Ya ce an kwato lita 121,035 na danyen man fetur da aka sace, tare da lita 19,650 na man dizel da aka tace ba bisa ka’ida ba (AGO), da kuma lita 7,140 na man kalanzir (DPK).

https://www.krmhausa.com/2025/06/sojojin-najeriya-sun-kashe-kwamandan.html

A cewarsa, sojojin sun kuma gano tare da lalata injinan da ake amfani da su wajen tace mai guda 25, ramukan ajiya guda 32, kwale-kwale guda 19, tankokin ajiya guda 40 da kuma ganguna 28.

Ya ƙara da cewa:
"An kuma kwato injina da bututun satar  mai da injinan hako mai, babura, wayoyin hannu da kuma motoci guda tara."

Baya ga haka, an cafke mutane 23 da ake zargi da laifukan sata, tare da kwato makamai da harsasai daban-daban daga hannunsu.

A wani bangare na aikin yaki da garkuwa da mutane da sauran laifuka, Kangye ya bayyana cewa daga 7 zuwa 8 ga Yuni, dakarun soji sun gudanar da samame a ƙananan hukumomin Okigwe da Aniocha da ke jihohin Imo da Delta. A yayin samamen, an kama mutane biyu da ake zargi da laifuka, tare da ceto wani mutum da aka yi garkuwa da su.

https://www.krmhausa.com/2025/06/babban-hafsan-sojin-kasa-coas-olufemi.html

An kuma kwato makamai, harsasai, wayoyin salula da babura daga hannun masu laifin.

Previous Post Next Post