Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Ambasada Ilya Umar Damagum, ya musanta jita-jitar da ke cewa yana shirin sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki, ta APC.
A wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman, Nuru Jos, ya fitar, Damagum ya bayyana rahotannin a matsayin shafcin gizo da karya kuma mara tushe har da 'kage daga wasu ‘yan adawa da ke da niyyar bata masa suna.
Rahotannin sun yi zargin cewa Damagum na shirin sauya sheka zuwa APC mai mulki a boye bayan karewar wa’adinsa a matsayin mukaddashin shugaban PDP na Kasa a babban taron jam’iyyar da aka shirya gudanarwa daga ranar 28 zuwa 30 ga watan Agusta na 2025.
Sai dai Damagum ya ce ba shi da wani shiri na barin jam’iyyar PDP, kuma bai shiga kowace yarjejeniya a boye da jam’iyyar APC ba.
Ya ce yana nan daram da Jam'iyyar PDP kuma yana ci gaba da aiki domin ciyar da jam’iyyar gaba.