Wani jirgin sama da ke kan hanyarsa zuwa birnin London ya yi hatsari a yau a birnin Ahmedabad da ke yammacin Indiya, inda mutane 242 ke cikin jirgin, kamar yadda hukumomin sufurin jiragen sama suka tabbatar, inda Kamfanin jirgin ya bayyana lamarin a matsayin hadari mai ban tausayi.
Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Indiya ta ce jirgin ya fadi ne a wajen harabar filin jirgin sama, inda aka tabbatar da cewa jirgin na dauke da mutane 242, ciki har da matuka jirgi biyu da ma’aikatan cikin jirgi guda goma.Ministan sufurin jiragen sama na Indiya, Ram Mohan Naidu Kinjarapu, ya bayyana cewa lamarin ya girgiza shi matuka kuma ya yi matukar bakin ciki. Ya umurci dukkan hukumomin jiragen sama da na agajin gaggawa da su dauki mataki cikin hanzari tare da yin hadin gwiwa.
Indiya dai ta fuskanci jerin manyan hadurran jiragen sama a baya, ciki har da hadarin shekarar 1996, inda jirage biyu suka yi taho mu gama a sama a birnin New Delhi, wanda ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 350.
Tags:
Labarai