Mai Horas Da 'Yan Wasan Poland, Michal Probierz, Ya Yi Murabus

Mai horaswan ƙasar Poland, Michal Probierz, wanda ke rikici da tauraron ɗan wasan gaba Robert Lewandowski, ya ajiye aikinsa.

A cikin wata sanarwa, Probierz ya bayyana cewa horar da ƙungiyar ƙasar shi ne burin sa a rayuwa kuma mafi girman girmamawa da ya taba samu a rayuwar shi.

Idan za’a iya tunawa, Lewandowski ya bayyana a ranar Lahadi cewa zai kaurace wa ƙungiyar muddin Probierz na matsayin mai horaswan ta, bayan da ya kwace masa kambun jagorancin ƙungiyar a matsayin kyaftin.

Previous Post Next Post