A wani muhimmin ci gaba, Sarkin Jordan Abdullah II da Firaministan Spain Pedro Sanchez sun halarci bikin sanya hannu kan wani shirin hadin gwiwa da ke shimfida tubalin sabuwar dangantaka ta dabarun ci gaba tsakanin kasashensu.
Wannan kawance na musamman zai hada bangarori da dama ciki har da tattalin arziki, cinikayya, al’adu, zamantakewa da tsaro. Haka kuma, an rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a fannin noma da wata yarjejeniya ta mika wadanda ake zargi da laifi tsakanin bangarorin biyu, a cewar rahoton Jordan News Agency.
A yayin ziyarar tasa a Madrid, Sarki Abdullah ya gana da Sarkin Spain Felipe VI, inda ya nuna godiya kan matsayin da Spain ta dauka na goyon bayan 'yancin Palasdinawa da kuma kokarinta na ganin an samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya. Ya yaba da matakin Spain na amincewa da kafa kasar Palasdinu tare da bayyana cewa Jordan na kokarin samun karin goyon bayan Turai ga shirin Larabawa na sake farfado da Gaza ba tare da tilastawa mazauna barin yankin ba.
Firaminista Sanchez ya bayyana Jordan a matsayin kasa mai muhimmanci wajen tallafa wa al’ummar Palasdinu, tare da jaddada bukatar kawo karshen yakin da ake ci gaba a Gaza.
Tawagar Sarki Abdullah ta hada da Mataimakin Firaminista kuma Ministan Harkokin Waje Ayman Safadi, Daraktan Ofishin Sarki Alaa Batayneh da Jakadiyar Jordan a Spain, Raghad Al-Saqqa.