Kafin wasan sada zumunta na Ƙasa da Ƙasa da za a buga ranar Juma’a tsakanin Najeriya da Rasha a filin wasa na Luzhniki, kocin Super Eagles, Eric Chelle, ya bayyana shirye-shiryen tawagarsa tare da bayani kan dalilan rashin wasu manyan ’yan wasa.
Chelle, wanda ya jagoranci Najeriya zuwa nasara a gasar Unity Cup da aka buga a birnin London, zai yi amfani da wannan wasa wajen ci gaba da gina tawagar tasa kafin fara muhimman wasannin neman tikitin shiga gasar AFCON da na cin kofin duniya na 2026.
Sai dai kocin ya bayyana cewa ba zai samu damar amfani da wasu fitattun ’yan wasa ba saboda dalilai da suka shafi kungiyoyinsu, rauni, da kuma matsalolin gudanarwa.
https://www.krmhausa.com/2025/06/stanislav-agkatsev-ya-bayyana-kungiyar.html?m=1
“Osimhen da Lookman ’yan wasa ne masu kwarewa da basira, amma yanzu lokacin hutun kakar wasa ne, kuma suna cikin wani mataki na yanke shawara kan makomarsu a kungiyoyinsu. Wannan ne dalilin rashin zuwansu,” in ji Chelle.
Sauran ’yan wasan da ba sa cikin tawagar Najeriya sun haɗa da Nathan Tella, Samuel Chukwueze, da Wilfred Ndidi.
"Nathan Tella, ba zai iya zuwa ba saboda matsalolin fasfo da biza. Samuel Chukwueze yana da matsaloli na iyali da yake bukatar warwarewa, yayin da Wilfred Ndidi ya samu rauni. Wadannan su ne dalilan rashin zuwansu,” in ji kocin.
https://www.krmhausa.com/2025/06/mai-horasa-da-kungiyar-kwallon-kafa-ta.html?m=1
Duk da wadannan kalubalen, Chelle ya bayyana kwarin gwiwar sa kan kokarin tawagarsa.
“Rasha na da kwararrun ’yan wasa masu karfi da kuzari. Sun fi amfani da karfi da saurin wajen yin wasa, kuma suna da kwarewa sosai.
Ya ce, Ina ci gaba da nazari kan dabarun da za mu yi amfani da su.
Ya kara da cewa, burinsu shi ne samun nasara.
“Kamar yadda aka saba a kowanne wasa, burinmu shi ne samun nasara. Ni da ’yan wasa da ma’aikatan tawagar duka muna da buri daya ne — mu lashe kowanne wasa. Mun san wasan ba zai zama mai sauki ba saboda kyau na kungiyar Rasha.”
Wannan wasa na ranar Juma’a zai kasance karo na farko da za a taba yin fafatawa tsakanin manyan kungiyoyin Najeriya da Rasha.
Ko da yake kungiyar Rasha ba ta buga gasa tsakanin ƙasa da ƙasa ba tun 2022, sun nuna kwarewa a wasan da suka yi na baya-bayan nan inda suka doke Zambiya da ci 5-0.