Kasashen Uzbekistan da Jordan sun samu nasarar zuwa Gasar Cin Kofin Duniya ta maza karo na farko a tarihi.
Uzbekistan ta samu gurbin ne da saura wasa daya a rukunin A na zagaye na uku na cancantar shiga gasar a nahiyar Asiya, bayan sun tashi kunnen doki 0-0 da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a ranar Alhamis.
Wannan sakamako ya sanya Uzbekistan a matsayi na biyu da maki da ba za a iya kaiwa gare ta ba – maki hudu a gaban UAE – lamarin da ya tabbatar musu da tikitin zuwa gasar cin kofin duniya ta shekara ta 2026. Wannan ya sanya su zama kasa ta biyar da ta samu gurbi, banda kasashen masu masaukin baki – Amurka, Mexico da Canada.
Dan wasan bayan Uzbekistan, Abdukodir Khusanov, ya koma Manchester City a watan Janairu, yayin da kyaftin din tawagar kuma ɗan wasan gaba, Eldor Shomurodov ke buga wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Roma.
Japan ce kasa ta farko ba daga cikin masu masaukin baki ba, in da ta cancanci zuwa gasar ta bana. Iran ma ta samu gurbi bayan yin kunnen doki 2-2 da Uzbekistan a watan Maris, yayin da New Zealand ta samu nasarar shiga a sabon gurbin da aka ware wa kungiyar Oceania.
Masu rike da kofin yanzu, Argentina, sun tabbatar da samun gurbin shiga gasar a ranar 25 ga Maris bayan wasan da Bolivia da Uruguay suka kara aka tashi 0-0 – wanda hakan ya sa tawagar Lionel Scaloni, ta zama ta farko daga Kudancin Amurka da ta samu gurbin gasar.