Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa a kalla mutane 871,000 ne ke rasa rayukansu a duk shekara sakamakon nesanta kansu da jama'a.
A cewar hukumar lafiyar WHO, daya daga cikin mutane shida a fadin duniya na fama da kaɗaici, wanda hakan kan iya janyo matsalolin lafiya.
Hukumar ta bayyana cewa halayyar nesanta kai da jama'a na kara barazanar kamuwa da bugun zuciya, ciwon zuciya, cutar sikari, damuwa, tashin hankali da kuma kisan kai.
WHO ta kuma lura cewa matasa masu fama da rayuwar kaɗaici na da kashi 22 cikin dari na yiwuwar samun sakamako mara kyau a makaranta idan aka kwatanta da abokan karatunsu, yayin da manya ke fuskantar kalubale wajen samun aiki ko kuma rike shi.
Ta kara da cewa tasirin wannan matsala ba ya tsaya kan mutum daya ba ne, domin yana janyo asarar biliyoyin kudi ga tsarin kiwon lafiya da kuma rage yawan ma’aikata.
Ɗaya daga cikin shugabannin hukumar, Vivek Murthy, ya bayyana matsalar nesanta kai da jama'a da cewa “wani rashin jin dadi ne da mutum kan ji a zuciyarsa idan dangantakar da yake bukata ba ta dace da wacce ya samu ba.”
Ya ce daga cikin dalilan da ke janyo hakan akwai rashin lafiya, karancin ilimi, talauci, rashin samun damar mu’amala da jama’a, zama kai kadai da kuma dogaro da fasahar zamani.
WHO ta bada misali da kasar Sweden, inda aka aiwatar da wata dabara don yaki da halayyar kaɗaici, kamar yadda Ministan harkokin zamantakewa na Sweden, Jakob Forssmed, ya bayyana.
Sweden ta amince cewa kewa ba matsalar mutum ɗaya ba ce kadai, illa ce da ke shafar al’umma baki ɗaya. Ana kuma kokarin samar da hanyoyin haɗin kai tsakanin al'umma a kasuwanni, gidajen cin abinci, unguwanni da kungiyoyi.
Ministan ya ce nan ba da dadewa ba za samar da katin ga Yara da Matasa da zasu dinga amfani dashi wajen ziyartyar wuraren nishadi da shakatawa
Mr Forssmed ya ce Sweden na shirin haramta amfani da wayoyin salula a makarantun gwamnati.