Masu sana’o’i a shataletalen titin Hotoro zuwa Farawa sun roki Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya duba makomar su tare da iyalan su bayan ganin alamar jan fenti da ke alamta tashin su daga wuraren da suke gudanar da harkokin su na kasuwanci.
Sun ce wannan shine wurin da suke neman na rufawa kai asiri, kuma kwatsam sai suka wayi gari da ganin wannan alama, lamarin da ya sa suka bukaci gwamnati ta samar musu da wani wurin da za su cigaba da kasuwanci, domin kaucewa zaman banza da rashin aikin yi.
Kana sun ƙara da cewa sama da shekaru goma suna gudanar da sana’o’i a yankin, wanda ke taimaka musu wajen kula da rayuwar iyalai da kuma gudunmawa ga tattalin arzikin jihar.
Tags:
Labarai