Saudiyya ta jagoranci jerin kasashen Larabawa da suka bayyana kakkausar suka ga hare-haren da Isra’ila ta kai a Iran, inda aka ga an kai farmaki kan muhimman wuraren da ke da alaka da cibiyoyin samar da nukiliyar kasar.
Rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila ta kashe babban kwamandan dakarun juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC), Manjo Janar Hossein Salami, tare da wani babban jami'in IRGC da kuma wasu masana nukiliya guda biyu.
Kasashen Oman, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Jordan da Qatar suma sun fito fili suka yi tir da Allah wadarai da matakin da Isra’ila ta dauka.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa:
“Masarautar na bayyana matukar Allah-wadanta da kuma kin jinin hare-haren Isra’ila babu kakkautawa da suka kai kan kasar Iran, wanda hakan ya saba wa ikon kasa da tsaron ta, kana kuma wani babbanabu ne na take hakkin kasa da kasa da kuma dokokin duniya.”